BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA
Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!Tambayoyi da amsarsu tare da Mallam Ibrahim Zakzaky na biyu
TAMBAYA: Akramakallahu na yi mafarki ana azabtar da ni da wuta. Na yi ta addu'a amma ba a daina ba har na farka. Ko me wannan yake nufi? Kuma wacce shawara Malam zai ba ni a kan haka? Daga Usman Mai Allo, Gashuwa.
SHAIKH ZAKZAKY: To, lallai ba ni da ilimi dangane da fassarar mafarki. Sai dai shi mafarki yana iya zama albishir ko garagadi. Wannan yana iya zama gargadi a gare ka. Saboda haka sai ka guji abubuwan da kake aikatawa wanda Allah ba ya so. Kuma ka roki Allah ya yafe maka. Wallahu a'alam.
TAMBAYA: Assalamu alaikum, nine dana ya yi laifi, na tashi hukunta shi, sai ya ji ciwo a sanadiyyar wannan hukuncin da na yi masa. Shin akwai diyyar da zan biya ne ko kuwa? Daga Aliyu Hasan Narayi, NITEL Maiduguri.
SHAIKH ZAKZAKY: E, lallai za ka biya diyya daidai gwargwadon jin ciwon da ka yi masa. Kuma sai a kai wa adilai su yi hukuncin, ba kai za ka yi hukuncin ba. Sai ka fid da daga cikin dukiyarka, ba dukiyarsa ba (shi yaron), sai ka biya yaron.
TAMBAYA: Allah gafarta Malam akwai diyyar da ake biya idan an buge dabba da abin hawa, ta mutu, ko ba ta mutu ba? Daga Aliyu Hasan Narayi, NITEL Maiduguri.
SHAIKH ZAKZAKY: Ma'abota hakki na wannan dabba din, akuya ce ko kare, to lallai in ganganci ne ba kuskure ba, to zai zama za ka biya. Alal misali, idan ya karye ne, aka nemi za ka biya wani abu domin a dora shi, ko a kai shi asibiti ko abin da ya yi kama da haka nan, to za ka dauki wannan dawainiyar. Amma wannan sai in ya zamana da ganganci ne ko da kuskure, ba bisa hadari ba. Alal misali kana ta tafiya, ba kai ka shige ma karen ba, ko dabba din ba, dabbar ta fado, to wannan zai zama babu komai.
TAMBAYA: Assalamu alaikum, mutum ne ya yi alwala, kafin ya yi sallah sai wani wanda ba musulmi ba ya mika masa hannu suka gaisa. Yaya matasayin alwalarsa? Daga Adamu Musa Garko, P.O. Box 140 Jada Adamwa.
SHAIKH ZAKZAKY: To, alwala tana nan sai dai idan ya tsargu dangane da rashin tsarkin shi wanda ya ba shi hannun, to sai ya wanke hannun.
TAMBAYA: Assalamu alaikum, mutum ne ya je yin sallama da iyayensa zai je taron harka islamiyya, to sai iyayen nasa suka ji tsoron azzalumai za su iya auka wa a wajen. Saboda haka sai suka hana shi. Shin ya tafi kawai ko kuwa dai ya tsaya? Daga Mukhtar ALMIZAN Malumfashi.
SHAIKH ZAKZAKY: To, iyaye na da hakki na biyayya a kan abin da bai sabawa na Allah ba. Har wala yau kuma kana da hakki na yin harkar addini, ko da iyayenka ba su yarda ba in shi ne mafita a gare ka. Wannan ya danganta da yadda kai ka ga wannan zuwa din kenan. Tana iya yiwuwa ya zama maslaha ka bi shawarar iyayenka din, tana iya kuma zama (kamar mu ba abin wata fassarar kamar wani yaki ne wanda ya zama lazim a yi). Amma dai ya danganta da matsayin abin da za ka je din ne. Misali in ya zama mai nema ilimi ne, kuma a nan ne kawai za ka samu wannan ilimin, to yana iya zama ka ga cewa, to lallai ko da hadari dai, in ma ka fada hannun azzalumai sun yi maka wani abu, to kana da ladan wannan.
TAMBAYA: Allah gafarta Malam nine nake bin bashi har lokacin fid da Khumusi ya yi, sai na fitar da khumusin wadanda nake tsammanin za su biya ni. Sai daya daga cikinsu bai biya ni ba, amma wadanda ban yi tsammanin za su biya ni ba, sai daya daga cikinsu ya biya ni. Kuma a daidai lokaci guda. Sai na kaddara cewa ai shi kenan. Sai bayan tsawon lokaci na yi tambaya, sai aka ce sai dai na koma can inda na kai Khumusin in yi bayani. Allah gafarta Malam mene ne hukuncin? Daga Muhammad Ghali Yahya.
SHAIKH ZAKZAKY: To dama tun farko ba za ka biya Khumusin abin da bai zo hannunka ba, sai abin da ya riga ya zo hannunka. Tun farko wato bashi za ka fitar da shi daga wanda kake bi daga cikin lissafin. Amma tunda kai ka yi amfani da fatawar kanka ka fidda ma na bashi, to sai mu dauka ya riga dai ya tafi, amma dai bai hau kanka ba da ma. Sannan kuma idan bashin da ya zo hannu din ya yi daidai da wanda bai zo hannu ba, to shi wanda ka fitar, wanda ba ka tsammani din ya tsaya a matsyinsa. In kuma da bambanci kai sai ka cika. In ko da ragowa, to lallai ba za ka je ka ce a ba ka ragowarka ba. Sai dai ka yi fatan Allah ya ba ka lada.
TAMBAYA: Ina so Malam ya yi mani bayanin yadda ake ciyar da miskini idan mutum ya sami matsalar da ta hana shi yin azumi. Daga Sadik Basiru Minjibir.
SHAIKH ZAKZAKY: To, hanyoyi ne guda uku; tufatarwa, idan namiji ne riga da wando, idan mace ce doguwar riga da murfin kai. Sai kuma ciyarwa, wanda yake nufin mutum ya ba da abinci dafaffe, wanda mutum zai ci ya koshi har da abin sha. Ko kuma ya ba da mudu guda na Annabi. Amma shi ana son wannan in zai ba da mudu ne ya nunka biyu, sannan kuma ya ba da abin miya. Amma wala'alla tufatarwar shi ya fi alheri ga mafi yawan miskinai, wadanda suka rasa tufafi. Na biyu kuma sai ya zama ba da kayan abinci, musamman ga ma'abocin iyali, wanda shi ma an yarda kana iya lissafin ma har da iyalansa. Misali in yana da mace daya da 'ya'ya biyu, za ka iya ba shi kason mutum hudu, amma in ka tabbatar da cewa zai ciyar da iyalin ne ba zai je ya sayar ne ya yi wani abin da kudin ba.
TAMBAYA: Mutum ne ya zubarwa da wata mata ciki ta hanyar yin allura, shin ko hukuncinsa daidai yake da wanda ya kashe rayayye mai lafiya? Daga Muntaka Liman Sabon birni, jihar Sakkwato.
MALAM ZAKZAKY: To hukuncin zubar da Tayi ne a kansa, wanda shi wannan hukuncinsa daban ne da kashe haifaffen yaro. Akwai hukuncin zubar da Tayi, ba sai na yi dogon bayani a kai ba, har da diyyarsa. A duba a muhallinsa.
TAMBAYA: Na ji ana cewa idan mutum ya saka abinci a baka kamar nama, sai ya fito da shi ya sake mayar da shi ya hadiye shi, ya haramta. Mene ne gaskiyar lamarin? Daga Muntaka Liman Sabon birni, jihar Sakkwato.
SHAIKH ZAKZAKY: To lallai ban san wani abu dangane da wannan ba. Sai kawai in shi yana ganin abin kyama ne. Ta yiwu mutane suna ganin abin kyama ne abin da ya fito baki a mayar da shi, amma dai ba wai haramci ba.
TAMBAYA: Ni mai sayar da littattafan addini ne, amma ina hadawa da littattafan soyayya. Shin meye hukuncin sayar da littattafan soyayya? Daga Yahya Mai littattafai Isa, jihar Sakkwato.
SHAIKH ZAKZAKY: To, idan abin da yake cikin littafin babu laifi da shi, to ba laifi ka sayar. Amma idan akwai batsa da wasu miyagun abubuwa a ciki, wanda yake kamar kana tallata shi ma wannan batsar ne, to ba zai halatta ba.
TAMBAYA: Shin ko ya halatta mutum ya yi 'brushing'(wanke baki da Makilin) alhali yana azumi? Daga Yahya Mai littattafai Isa, jihar Sakkwato
SHAIKH ZAKZAKY: To, lallai mun taba amsa wannan tambaya din. Muka ce ba ma ya halatta bane har ma yana da kyau, don warin bakin mai azumi da aka ce ya fi kanshin Miski ba ana nufin kazantar baki ne ba. Ana nufin hamami ne da kan fito daga ciki sakamakon rashin abinci. Yakan rinka wani irin kanshi saboda daga hanji yake fitowa. Amma ta baki yake fitowa shi ya sa aka kira shi 'faikh'. Amma a Larabci ma ba an ce warin baki bane, Hausawa suka ce masa warin baki, amma 'faikh' aka ce masa, wanda kamar tururi ne yake fitowa daga uwar hanji sakamakon ba komai a ciki. Saboda haka wanke baki da wannan ba zai yi komai ba matukar mutum ba zai hadiye ba. Kasantuwarsa yana da dandano bai cutar ba. Da zaki yake ko daci, ko ma wane ne, bai cutar ba, matukar bai hadiye ba.
TAMBAYA: Mutum ne dan kasuwa mai shago kusa da masallaci kuma sauti na kai masa. Shin ko ya halatta ya rinka bin jam'in sallah daga nan? Daga Yahya Mai littafai Isa jihar Sakkwato.
SHAIKH ZAKZAKY: A'a bai halatta ba. Don daga cikin ka'idar bin jam'i har sai idan ka sadu da sahu da kirjinka ko da kafadarka. Saboda haka sai dai idan sahun ne ya shigo har shagonsa jama'a suka bi ta cikin shagon nasa, to yana iya yin haka nan. Amma in ba haka ba, to lazim ne ya sadar da sahu. Idan ya zama da tazara tsakanin sa da masallaci, to shi sallarsa ba ta inganta ba.